<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>567</hymn_number>
<title>Yesu Gaban Kayafas LW567</title>
<lyrics>[V1]
 1) Yesu gaban Kayafas, Yesu gaban mayan malamai,
 Yesu gaban Bilatus, domin ya fanshe ni.
 An yi masa bulala, an yi masa ba'a,
 Yesu ya sha wahala, domin ya cece ni.

[V2]
 KORUS
 Yesu ya sha wahala (3x)
 Domin ya fanshe ni.

[V3]
 2) An tofa masa miyau, da babbakun magana.
 Yesu ya ɗauki giciye domin ya fanshe ni.
 Yesu a bisa giciye, ya zub-da jininsa,
 Yesu a cikin Kabari, domin ya cece ni.
 Korus

[V4]
 3) Yesun mu ya tashi da rai,
 Yesun mu yana da rai
 Yesu ya hau cikin sama
 Domin mu sami rai

[V5]
 4) Ka tuna domin ran dawowarsa
 Gama ranar nan ƙarshe ne. Bass : &quot;Ƙarshe ne&quot;
 Ƙarshe ne, ƙarshe ne,
 Gama ranan na ƙarshe ne.
 Korus

[V6]
 5) Ka tuna da miyagun ayyukanka daina su
 Kamin Yesu ya dawo. Bass:&quot;A ƙarshe
 Ayyukan miyagu, ka daina su
 Kamin Yesu ya dawo.
 Korus

[V7]
 6) Ka tuna randa za ka Kabari
 Gama ranan nan ƙarshe ne.
 Ƙarshe ne, ƙarshe ne
 Ran da za ka Kabari, ƙarshe ne.
 Korus</lyrics>
</song>